An kafa Gidan Karatu ne a shekarar 2018, saboda fahimtar cewar akwai ƙarancin kafafen rubutu da karatun harshen Hausa na zamani musamman a yanar-gizo.
Zamani ya canza, kuma wannan kyakkyawar al’adar Bahaushe ta karance-karancen litattafanmu, don assasa fahimtar al’adu, addini, samun kwanciyar hankali da natsuwa, ta faɗi warwas!
Gidan Karatu zai yi ƙoƙarin haɓɓako da wannan al’adar, insha Allah.