Marubutanmu

Atabo Mohammed

Abuja

Atabo Mohammed mutumin Kwantagora ne, jihar Neja. Salon rubutunsa nada jan hankali ta yadda duk ka fara karatu ba zaka ajiye littafi ba sai ka gama.

Yana da son litattafa masu zurfin hikima da ma’ana.

Bayan Iskar Hunturu, litattafan da ya rubuta sun hada da Labarin Shekarau Gardo da Birnin Masana Hikima (ga hotunansu nan a kasa)

Mallam Mohammad na zaune ne a garin Abuja.

Li Peifu

China

An haifi Li Peifu a Xuchanga Jihar Henan ta ƙasar Sin a watan Oktoba, a shekarar alif ɗaritara dahamsin dauku (1953). Yafara wallafa ayyukansa a cikin alif ɗari tara da saba’in da takwas(1978)

Duniya Labari wanda ya kasance littafi mafi shahara a littatafansa kuma shine na k’arshe a jerangiyar littatafan da yayi musu laƙabi da Littafi na Ɗaya, Dana Biyu, Danauku (PlainsTrilogy)

Kuna sha'awar wallafa littattafanku da mu?