Iskar Hunturu

Wani lokaci, ba ruwan rayuwa da sassauci!’

Ga masu son litattafan badaƙala, wannan labarin naku ne!

Atabo Mohammed ya tara mana jini a farata da sabon littafinsa, Iskar Hunturu, inda ya bada labarin ruguntsumin da ƙawaye biyu― Mariya da Zainab― suka faɗa, wajen yunƙurin zubar da cikin da Zainab ta ɗauka dab da kammala karatun jami’a.

Zainab ta gummace ta rasa ranta da ta je da cikin gida. Tare da Mariya, suka nemi wajen ɓuya, inda za su yi abinsu, su gama cikin sirri ba tare da duniya ta sani ba.  Sai dai basu gama fahimtar al’amarin ba balle su hango hatsarin da rayuwar mai cikin zata faɗa...

Zainab ce ta sha maganin, amma Mariya aka bari da jin uƙubar da Zainab ta shiga: duk lokacin da Mariya ta rufe ido, sai ta ji ƙugnin Zainab mai ban tsoro cikin kanta, sai ta tuna da tafkin jinin da Zainab ta zubar, sai ta ji ƙunar shauƙin azabar fitar cikin, sai kuma ta tuna da tashin hankalin da ya damƙe ta daidai lokacin da numfashin Zainab ya ɗauke..
Labarin na nuna irin matsalolin da matasan zamani ke shiga dalilin sakaci wajen yin zaɓin da suka dace a rayuwa, musamman ga masu ilimin zamani. A zamanin nan ana alaƙanta wayewar mutum da Iliminsa. Sai dai kuma siffar da wayewar ke ɗauka dangane da assasa tarbiyya, ita ce matsalar.

Duk da cewa iyayen Zainab na da tabbacin cikar tarbiyar da suka bata, goguwar zamani ta sa ta yi zaɓin da bai dace ba. Hakan ya jefa ta cikin matsalolin da ƙawarta Mariya ta yi ta fama dasu.

Bayan iyaye sun bada tarbiyya, duniya ma sai ta bada tata ko an ƙi ko an so— kamar yadda mahaifin Mariya ke yawan faɗa. Sai dai kuma tarbiyyar duniya wani lokaci, ba sassauci, ba tausay; Zainab da Mariya sun tabbatar da hakan, da suka ga halaka gabansu tana jira.

An bada labarin ta yadda zai iya jawo hankalin mai karatu cikin sawun Mariya da Zainab, ya auna hankula da kaifin tunaninsu, yaga ko abubuwan da suka aikata zai yi tasiri wajen warware matsalolinsu.

Muna fatan cewa bayan nishaɗantarwa, mai karatu zai ƙara fahimtar rayuwar matasanmu a yau, dangane da yadda yalwar ilimi da goguwar zamani ke ja-in-ja cikin rayuwarsu.

Bayani Kan littafin Daga Bakin Marubucin, Atabo Mohammed.

Ga tsokacin da masu karatu suka yi kan littafin

“Gaskiya, littafin ya siffanta tashin hankalin da ƴan manta ke shiga idan suka yi ciki a waje, musamman ma waɗanda suka fito daga gidan mutunci. Matsalar da Zainab ta shiga akwai ban tsoro; ga tunanin shiga kunyar iyaye da na duniya, da ma na lalacewar rayuwarta gaba ɗaya!”
Inji Mairo Usman
Daga Kwantagora
“An yi tunani mai zurfi cikin littafin, musamman wajen warware sarƙaƙƙiyar matsalar. An kuma zayyana hanyoyin da mutum zai iya duban matsalolinsa da wata fuska ta daban don warware su.”
Inji Sharhabila M Idris
Daga Kaduna
“Labarin ya nuna ainihin siffar ƙawance na asali wanda ya kamata ace mata sun lura da ita. Ba kowa ce zata iya abin da Mariya ta yi ba: ta san aibin Zainab, ta kuma san hatsarin da ita kanta za ta iya shiga idan bata yunƙura ta san nayi ba, amma ta jajirce!”
Inji Hannatu Isah
Daga Kano

Fara Karanta Littafin Kyauta!

Ku fantama cikin labarin kai tsaye! Amma kafin ka iya bude shafin, sai kunyi ragista. 

Bayan kun yi, ku latsa ‘Koma Shago’, littafin na jiranku can.

Labarin bai ƙare ba!

Kuna Gama karatun littafin farko, sauran na jiranku.