Description
Bayan shekara da shekaru da aka yi a ƙasar Sin ana rayuwa a bisa aƙidar Gurguzu inda gwamnati ke da mallakar zuba jari da kasuwanci, an zo an samu sauyin aƙida wadda ta bai wa mutane ikon kafa masana’antunsu da kuma zuba jari.
A cikin sauyin nan ne kuma aka bai wa ‘yan ƙasashen waje ikon zuba jari ko kuma su kafa kamfanonin haɗin gwiwa da ‘yan ƙasa.
Mutane sun yi amfani da wannan daman saboda cimma buƙatunsu.
A cikin waɗannan mutane, akwai Kamal wanda ya yi amfani da ilmi da basira ya mallaki dukiya, amma rashin wadatar zuci ya kai shi ga kashe kansa.
Akwai Diu, aminin Kamal tun daga makaranta, wanda ya yi taka-tsantsan har ya zo ya mallaki abin da Kamal ya kasa samu a sauwaƙe.
Ga kuma Fan wanda ya yi shekara da shekaru yana rayuwarsa bisa tafarkin doka da oda, amma daga ƙarshe soyayya ta kai shi kurkuku.
Wannan labari ne da yake nuna irin halin da mutane suka samu kansu ciki lokacin sauyin aƙida wadda ta tabbatar da cewa abubuwa sun canju.
Reviews
There are no reviews yet.