Description
Atabo Mohammed ya tara mana jini a farata da sabon littafinsa, Iskar Hunturu (Wallafar Gidan Karatu), inda ya bada labarin ruguntsumin da ƙawaye biyu― Mariya da Zainab― suka faɗa, wajen yunƙurin zubar da cikin da Zainab ta ɗauka dab da kammala karatun jami’a.
Zainab ta gummance ta rasa ranta da taje da cikin gida.
Tare da Mariya, suka nemi wajen ɓuya, inda za su yi abinsu, su gama cikin sirri ba tare da duniya ta sani ba. Sai dai basu gama fahimtar al’amarin ba balle su hango hatsarin da rayuwar mai cikin zata faɗa…
Zainab ta sha magani, amma Mariya aka bari da jin uƙubar da Zainab ta shiga― ƙugi mai ban tsoro; duk Mariya ta rufe ido, sai ta ga tafkin jinin da Zainab ta zubar, sai ta ji ƙunar shauƙin azabar fitar cikin, sai kuma ta tuna da tashin hankalin da ya damƙe ta daidai lokacin da numfashin Zainab ya ɗauke…
Reviews
There are no reviews yet.