Marhaba

Salamu alaikum;

Muma marubuta ne kamar ku. Wasu daga cikinmu sun share fiye da shekara goma suna harkar rubuce-rubuce da wallafa litattafai. Hakan ya sa sun samu kyakkyawar fahimtar yadda harkar take, da kuma abubuwanda marubuta kansu za su so game da ayyukansu.

Tabbatar da marubuta sun samu waɗannan abubuwan yasa muka kafa Gidankaratu. Kuma muna so mu haɗa hanu gaba daya mu cimma wannan burin. 

Abubuwan Da Muke Samarwa Marubuta

icon-1-2.png

Wallafa Litattafai

Muna wallafa litattafai a fagen nan ta yadda masu karatu za su ga litattafanku, su saya, su karanta cikin natsuwa, su yi tsokaci kai, su bashi tauraron yabo wanda zai ƙarawa littafin aminci ya kuma bunƙasa kasuwarsa Sannan litattafan zasu shiga su kuma tsaya yanar gizo ta yadda za a iya binciko sua kowane lokaci.

icon-7.png

Manhajar Karatu;

Bincike ya nuna cewa mafi yawan masu karatu a yanar gizo na duniya baki ɗaya, sun fi so su shiga fagen da aka ajiye litattafai ko mujallu musamman don karatu; hakan zai basu kwanciyar hankali, ya kuma haɓɓaka shauƙin son karatu. Wannan ne takamaiman fa’idar manhajar Gidankaratu. 

icon-2.png

Kariya Da Tsaro

Bugu da ƙari, mun tsara manhajar ta yadda litattafanku zasu samu kariya ta musamman na ba wanda zai iya ba wani littafin, sai dai wannan ya saya. Hakan zai sa marubuta su ci gajiyar aikinsu.

Kafin Ku Aiko Da Littafi

Kafin ku aiko, muna so ku fara karanta Dokoki da Sharuɗɗan Gidan Karatu tukun. Hakan na da muhimmanci wajen fahimtar yadda muke aiki, kar azo a samu matsala gaba.

Dagan nan kuma, sai ku duba Kwantirage domin sanin daidaita tsarin cinikayyarmu. Idan an amince, sai a ɗora littafi

Ku Latsa  rubutun da ke kasan hotunan nan.

Ana Neman Karin Bayani?

Account Dina

Dandali

Litattafai

Shago